Rekaman ini tidak melaporkan media yang dapat diputar untuk video 7656498744711449877; metadata publik di bawah tetap diindeks.
Statistik video
Jumlah publik dari pembaruan terakhir.
- Tayangan
- 9.355
- Suka
- 506
- Komentar
- 16
- Dibagikan
- 5
- Disimpan
- 112
- Interaksi
- 5,63%
- Durasi
- 0 dtk
- Diposting
- 28 Jun 2026
Wawasan video
Video TikTok @hikimadaily “KUSKURE 6 DA NAYI A SHEKARUNA NA 20 (INA FATAN KAI BA ZAKA YI SU BA) Na karshe yana da Mahimmanci amma sai kayi dogon nazari... A matsayina na wanda ya tsallako kogin da kuke gab da shiga, akwai wasu darussa da rayuwa ba ta koyar da kai sai ka biya da abu mafi tsada shine lokacinka. Ba na faɗar wannan don nadama, a'a, ina faɗa ne a matsayin darasi, don in miƙo muku taswirar da za ta taimake ku ku guji wasu ramuka a tafiyarku. 1. DARASI AKAN LOKACI: A shekaruna na 20, na ɗauki lokaci kamar iska ce da ake shaka,bata ƙarewa. Ashe lokaci jari ne da aka ba kowa daidai gwargwado. Na koyi cewa kowace rana da ta shuɗe, wani babi ne na littafin rayuwarka da ka rubuta ka gama, ba za ka taɓa iya gyara shi ba. 2. DARASI AKAN ABOKAI: "Kowa madubin abokinsa ne." Wannan maganar ban gane ta da gaske ba sai da na ga yadda abokai ke iya gina mutum ko su rushe shi. Na koyi cewa zaɓan abokan tafiya ya fi saurin tafiyar muhimmanci. Ka zaɓi waɗanda za su zama madubin da zai nuna maka girman da za ka iya kaiwa. 3. DARASI AKAN DUKIYA: A wancan lokacin, na ɗauka cewa darajar mutum tana cikin abin da ya mallaka. Na koyi cewa darajarka ta gaskiya tana fitowa ne daga abin da ka GINA, ba abin da ka KASHE ba. Ka gina kwarewa, ka gina sana'a, ka gina hali, wannan ita ce dukiyar da ba ta ƙarewa. 4. DARASI AKAN LAFIYA: Jikinka shine gidan da ranka yake zaune. A lokacin ƙuruciya, na yi wa wannan gidan riƙon sakainar kashi. Na fahimci cewa idan gidan ya fara rushewa, duk wani abu da ke ciki zai shiga matsala. Ba za ka iya neman arziki ba idan ba ka da lafiyar da za ta ɗauki nauyin aikin. 5. DARASI AKAN AIKI: Na yi ta jiran "lokaci mai kyau" ya zo, ashe babu wani lokaci mai kyau kamar YANZU. Na jinkirta fara wasu abubuwa saboda tsoron faɗuwa. Daga baya na koyi cewa babbar kasawa a rayuwa ba ita ce ka faɗi ba, a'a, ita ce kada ka taɓa gwadawa kwata-kwata. 6. DARASI AKAN ZUCIYA & SOYAYYA A lokacin ƙuruciya, na ɗauka cewa soyayya tana bukatar ka sadaukar da komai. Na ɓata lokaci, na kashe 'yan kuɗaɗena, na kuma ajiye wasu daga cikin burikana a gefe domin wata mace da batasan darajar sadaukarwar ba. Daga baya na koyi cewa, a wannan matakin na rayuwa, soyayya ta gaskiya tana taimaka maka ka GINA kanka ne, ba ta RUSA ka ba. Mace ta gari za ta taimaka maka ne ka gina daular ka, ba za ta zama sanadiyyar rushewarta ba. Sako Na Ƙarshe Zuwa Gare Ka: Ina miƙo muku wannan taswirar ne ba don ku ji tsoron kuskure ba, a'a, sai don ku guji ramukan da na taɓa faɗawa. Rayuwarku tana hannunku. Ka gina rayuwar da za ka yi alfahari da ita gobe. "Da ace littafi ba ya canja rayuwa, da masu kuɗi ba za su ci gaba da karantawa ba." Mutane da yawa suna cewa suna son su canja rayuwarsu. Amma kullum abu ɗaya suke yi. Suna kallon bidiyo na sa'o'i, amma suna ganin kuɗin littafi ya yi musu yawa. Ka tambayi kanka... Shekara ɗaya daga yanzu, rayuwarka za ta bambanta da ta yau? Idan amsarka ita ce "Eh", to dole ne ka canja abin da kake ciyar da kwakwalwarka. Littattafanmu ba na nishaɗi ba ne. An rubuta su ne domin su koya maka yadda za ka: • Yi tunani irin na masu nasara. • Fahimci mutane da rayuwa. • Gina ƙarfin zuciya. • Daina tsoron fara abu. • Inganta kasuwanci da rayuwarka. Ka tuna... Mutum zai iya rasa kuɗi ya sake samun su. Amma lokacin da ya ɓata ba zai sake dawowa ba. Kada ka jira sai rayuwa ta wahalar da kai kafin ka fara neman ilimi. Ka fara yau. Domin shekara mai zuwa, za ka yi godiya da ka yanke wannan shawarar. Idan kana son samun littattafanmu na PDF, 09030805886 ka aiko mana da saƙo a WhatsApp. Canjin rayuwa yana farawa da shafi na farko.#viral #fouryou #views” memiliki 9.355 tayangan, 506 suka, 16 komentar, 5 kali dibagikan dalam metrik publik yang dicatat indeks ini. Itu setara tingkat interaksi sebesar 5,63% (suka, komentar, dan bagikan dibagi tayangan). Video ini diposting 4 bulan yang lalu dan berdurasi 0 detik. Video ini telah disimpan 112 kali.
Data per 16 Okt 2026 (UTC), dari pembaruan publik terakhir yang dicatat indeks ini.
- Pengikut
- 35.507
- Mengikuti
- 3
- Suka
- 329.483
- Video
- 327
Hashtag di video ini
Tautan tetap berada di dalam indeks ini.
Pertanyaan umum
- Berapa tayangan video TikTok ini?
- Data yang diindeks di sini mencatat 9.355 tayangan, 506 suka, dan 16 komentar.
- Siapa yang memposting video TikTok ini?
- Video ini diposting oleh @hikimadaily, yang ditautkan dari halaman ini.
- Berapa tingkat interaksi video TikTok ini?
- Dari metrik yang dicatat, tingkat interaksinya adalah 5,63% (suka + komentar + bagikan dibagi tayangan).
- Kapan video TikTok ini diposting?
- Video ini diposting pada 2026-06-28, 4 bulan yang lalu.
- Hashtag apa saja yang dipakai di video ini?
- Data yang dicatat menautkan 3 hashtag, dimulai dari #fouryou.